Tsutsar nama Book 2

Tsutsarnama Part 3 Book 2

This entry is part 3 of 3 in the series Tsutsar nama Book 2

Typing📲

🐛TSUTSAR NAMA….!!🐛
(Itama nama ce)

𝑩𝒊𝒍𝒚𝒏 𝑨𝒃𝒅𝒖𝒍𝒍 𝒄𝒆🤙🏻

𝑩𝒐𝒐𝒌 𝒕𝒘𝒐
𝑷𝒂𝒈𝒆 𝒕𝒉𝒓𝒆𝒆

…….Tun ina sallan shigowar doctor biyu. Sai dai ganin ban idar ba yana komawa. A na ƙarshe suka shigo su biyu dai-dai na idar ina zaune kawai nayi tagumi cikin dogon nazari da son sanin a ina nake wai. Jin muryar da banyi zato ba kasancewar nasan na kuɓuta daga garesu yasa na ɗago da sauri. Shi ɗinne kuwa. Wato yaron mugun nan Maash. Ganin yanda ina ɗagowa ya duƙar da nasa kan ƙasa kamar wani munafuki ya sani cigaba da kallon nasa kawai. Doctor ne ya katseni da tambayar yaya nake jin jikina yanzu. Cikin janye idanuna na amsa masa da Alhamdullah. Ya nuna jin daɗinsa kafin yay min nuna da mutumin nan. “Now you will get all the answers to your questions from him. I will send a nurse with your medicine. If you eat, she will give you.” daga haka ya juya ya fita. Shiru ɗakin ya ɗauka kusan na minti ɗaya, kafin a ƙufule cikin dasashjiyar muryata mai nuni da banda lafiya na furta, “Ya akayi na dawo gareku? Ina ne nan kuka kawoni?”.
        Sake duƙar da kai yayi kamar mai tsoron bani amsa, sai kuma a hankali ya furta, “Kiyi haƙuri nan asibiti ne. Yaya jiki?”.
     Wani irin takaici ne ya ƙuleni, dan haka cikin sake zafafa harshe na amsa shi da, “Ba ruwanka da jikina. Kaje ka sanar ma wanda ya aikoka yasa likitan nan ya sallaman. Sannan ku fita a sabgata. Idan ba haka ba zan sakaku nadama da dana sanin sani na. In ba hakaba zan tabbatar muku TSUTSAR NAMA ITAMA NAMA CE”. Daga haka na yunƙura a hankali na miƙe, ko inda yake ban sake kallo ba na koma saman gadon. Dai-dai nan Nurse ɗin nan ta dawo…

KANO.

  A matuƙar tashin hankali zuciyar Mamyn su Mansoor ta gama shiga. Dan suna isowa asibitin ta farfaɗo ita. Amma Mansoor kusan awani uku kenan likitoci na tare da shi ba kuma su musu bayanin komai ba. Sai dai faman kaiwa da komawa suke a tsakanin ɗakinsa zuwa ofisoshinsu. Tun tana hawaye har ma sun ƙafe ta koma na zuci. Nadama take ji na sake shigarta akan abinda ta aikata. Lallai tayi dana sanin biyema shawarar ƴar uwarta. Inama zata iya maida hannun agogo baya. Data goge komai da yake a yanzu da maida baya data shuɗe. Dan har ga ALLAH Mansoor shine ɗa mafi soyuwa a zuciyarta. Kodan tasha matuƙar wahala ne a yayin haihuwarsa, ko kuwa dan kamanin da yake da mahaifinsa. Sam bazata iya jure rasashi ba. Dan bazata taɓa yafema kanta ba.
       “Mamy dan ALLAH ki zauna ki huta, in sha ALLAHU ɗan uwana zai tashi. Kinga kema fa ba lafiyar ne da ke ba”. Attahir ne mai maganar cikin tsantsar damuwa ganin yanda Mamyn tasu ke faman kai kawo ga hannunta dafe da kanta. Yasan komai zai iya faruwa da ita, dan bata gama dawowa dai-dai ba ta fito a ɗakin da aka kwantar da ita. Anyi-anyi kuma taƙi ta koma dole aka haƙura aka barta. Dan Dad ɗin su ma haushin dagiyar tata ya sashi komawa can gefe ya zauna kawai bai sake kulata ba.
         “Attahiru bazaka gane ba. Nasan bazaka fahimta ba. Barni kawai kaji. Barni da abinda ya dameni. Ni da kaina na jefa rayuwar yarona a bala’i. Da nasan haka zata kasance da ban aikata ba. Da ban hanashi aurenta ba. Attahiru idan na rasa Mansoor nima zaku rasani ne wlhy”.
     “Dan ALLAH Mamy ki daina faɗa. In sha ALLAHU bazamu rasaki ba. Ki kuma daina zargin kanki kowa baya wuce kuskure ai. Mansoor zai samu sauƙi. Ki masa addu’a”.
     Kuka mai nauyi ta sakar masa tana ƙoƙarin dafe bango saboda jirin dake neman yaddata taji ya kwasheta. Da sauri yayi kanta ya riƙota. Da taimakonsa suka zauna yana jera mata sannu. Dai-dai nan shima Dad ɗin su ya taso, hakama ƙannensu da suka haɗe kai gefe suna kuka. A ruɗe duk suke tambayar miya faru, sai da ta ɗago ta ce musu ba komai sannan suka shiga sauke ajiyar zuciya. Hakan sai yay dai-dai da fitowar amintaccen likitansu Dr Gana. Kamar waɗanda aka zabura duk suka miƙe garesa har Mamy. Har rige-rigen tambayarsa yaya Mansoor suke yi. Shiko ya ɗan bisu da kallo cikin damuwa. Sai kuma a hankali ya furta, “Alhaji idan babu damuwa na ganka a office mana. Amma Hajiya tai zamanta Please”.
       Tsantsar tashin hankali ne ya bayyana a fuskokinsu. Yayinda Mamy ta fashe da kuka sauran ƙanensu na tayata. Shi kansa Dad ji yay ƙafafunsa sun masa matuƙar nauyi. Haka shima Attahir ya gagara tashi har sai da doctor ya sake musu magana sannan. Attahir ne ya fara jarumtar miƙewa, sannan shima Abban ya tashi suka nufi office ɗin su biyu kowanne na jin zuciyarsa na bugawa da sauri-sauri tamkar zata faso ƙirazansu ta fito waje…..

       Ni kaina Bilyn ku zuciyar tawa bugawa take. ALLAH yasa dai ba rasa Mansoor mukai ba😭😭🙆.

ABUJA

       ★Sosai na birkicema likitan nan akan nifa sai nasan a inda nake. Hankalinsa ya tashi, dan ya tabbatar min in har ban kwantar da nawa hankalin ba aikinsu zai iya komawa baya. Ganin fa ba saurarensa zanyi ba ya sanar min in a Abuja ne cikin MAASH HOSPITAL.
      “Abuja?!”.
    Kansa ya jinjina min da sauri. “Yes, yes. You were brought from our branch in Kano. Once you have finished receiving the medicine, you will return. Please calm down”
    Rasama mi zance masa nayi, sai kawai nayi shiru ina kallon PA da suka shigo kusan tare. Shi doctor ya zata na fahimcesa ne, dan haka ya sauke ajiyar zuciya da cigaba da kwantar min da hankali. Ko kulashi ban sake yi ba. Har ya gama ɓaɓatunsa ya fita. Ɗauke idanu nai da ga kan PA ina mai cije lips ɗina da ƙarfi. Na fahimci waɗan nan mutanen so suke sai mun kai matakin ƙarshe da su. So suke sai na bijire ma maganar Yaya Musaddiq da Mansoor. So suke sai na musu fallasar da zata ruguza dukkan tanadinsu. Kamar PA ya fahimci mi nake ayyanawa a raina. Takowa yay ya ƙaraso gaban gadon ya ajiye ledar hannunsa. Kafin ya ciro wayarsa a aljihu yay ƴan danne-danne batare da yace komai ba ya ajiye min saman table da akai crossing a tsakiyar gadon da magunguna a kai da dama sune Nurse zata bani na birkice musu. Harara na ɗago zan watsa masa sai idanuna suka sauka akan fuskar wayar. Tamkar waccan ranar yanzun ma tar-tar nake ganinsa. Yanda ya kafeni da shegun idanunsa kaifafa kalar na maguna ya sakani sake ɗaure fuska tare da ƙarasa antayawa PA ɗin nasa hararar da nayi niyya. Sai dai ashe shi harma ya fice ya barni da wayar. Wani irin takaici ne ya sake ruƙunƙumeni. Dan haka na rumtse idanuna da ƙarfi ina jin matuƙar zafi a raina. Kafin na buɗesu gaba ɗaya a fusace kan wayar. Shiko shiru yay kawai yana kallona da kaifafan idanunsa da nake jin tasiri su har a cikin jinina. Duk da yanda nake jin tasirinsu ban janye nawa dake masa kallon tsana da takaici ba. Cikin kaushin harshe da disashiyar muryata ta marasa lafiya na furta, “Kai ko akwai zuciya a ƙirjinka?”.
        Shiru babu alamar zai tanka min, sai ma janye idanunsa da yay a wani kalar slowly ya maida kan laptop dake gabansa. Dan alamu ya nuna kamar a study table yake zaune. Cikin sake jin wani sabon baƙin cikin na kai hannu saman kaina dake sara min. Fahimtar bazai amsa min ba ya sani cigaba da faɗin, “Anya kai Musulmi ne?”.
      Cak ya tsaya daga barin abinda yake yi, dan haka ya ɗago muna kallon juna cikin ido, idanunsa sun wani kaɗa blue ɗin gwaiduwar tsakkiya ta ɓace ta zama siririya like mage sak. Zamansa ya gyara na ƙasaita da isa da ke tabbatar da shi matsayin ingarman namiji, ga wani irin shegen kwarjini da nake ji ya mamaye ɗakin har kamar na matsu kai kace a gabana yake mayen. Ganin haka ya sakani cigaba da maganata batare da na damu da duk abubuwan dake tattare da shi ɗin ba.
       “Idan har kai musulmi ne bana jin kasan HARAMCI da HALLACIN dake cikin dokokin addinin musulunci. Idan kuma har da zuciya a ƙirjinka tabbas bata masu IMANI bace. Ina mai baka shawara kada kai wasa da wuta a tafin hannunka, dan wutar da UBANGIJI zai ladabtar da ma’abota bijirewa ta ninka wadda ake girka maka shinkafa a duniya kaci sau dubu bisa dubu. Idan baka sani bane zan faɗa maka a yanzu ni ɗin MATAR WANI CE. igiyoyin AURE ne a kaina ba igiyoyin ɗaure dabba a turken turka ba. Kaji tausayin kanka, da gujema saɓama UBANGIJI ka maidani inda ka ɗakkoni gidan aurena hannun MIJINA da IYAYENA.”
          “Idan nan ne GARIN AUREN ni ne MIJIN kuma fa?”. Ya faɗa cikin wata iriyar muryar dakiya da gizago mai tsarga zuciya. Dan yanda sautin amon muryar tasa da kaifinta ya tasirantar da furucin nasa a tsakkiyar kaina kaɗan ya rage zuciyata bata ɓullo ta bakina ta fito ba. Amma duk da hakan sai ga tari mai ƙarfi ya sarƙe min numfashi. Gaf-gaf jikina dake a cikin yanayin rashin ƙarfi ya fara rawa. Bamma san lokacin da bakina ba ya furta “MIJI?!”. Sai kuma kaina yay wani irin masifar sarawa da ban taɓa ji ko tsinkayen irinsa ba. Ga nauyi da idanuna sukamin har inajin jijiyarsu na ja kamar za’a fincike min su. In dai har wannan ake kira hawan jini to tabbas ya sameni kuwa a yanzun nan. Dan ƙirjina kansa yay wani irin nauyi. A karo na biyu hankalina ya sake neman barina. Nai yaƙin maidosa jikina tare da ɗagowa ina kallonsa domin son tabbatarwa. Amma a maimakon amsa ma da nake buƙata garesa hankalinsa kwance yake cigaba da aikin gabansa. Wani irin kallo nake masa mai kama da firgici, yayinda shima ya zuba min nasa cat eyes ɗin cikin yanayin i don’t care tamkar zai cinyeni da su.
Cike da salon izza da ƙasaita ya wani sake tsuke fuska da yamutseta sannan ya furta, “Har yanzu kina da sauran dama. Domin guri bai ƙure miki ba na komawa inda kika fito. Ki bama yarona video ko fadar inda yake a ɗakko gobe ki koma garinku. Saɓanin hakan cigaba da dawwama ƙarƙashin mulkin mallakar Maashhhh. Ke baki mori rayuwar taki ba. Ba kuma ki iya yin komai akan abinda kike tunanin iyawa ba”………✍️

Yayanmu Barka da salla, ban sani ba ko a duniyarku kunyi azumin kuma🥱👩🏻‍🦯.

Masoya ina ƙara gaya muku kada ku bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR ta 2024 babu ku. Dan wannan karon komai fa na musamman ne. Sabuwar Shekara, sabon zubi da babu irinsa.

MARABA DA LALE GA MASOYAN ZAFAFA BIYAR💖💯💖ALLAH YA KARA ARZIKI… ZAFAFA BIYAR NAKU NE💃

ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏

Series Navigation<< Tsutsarnama Part 2 Book 2
Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *